Coronavirus: Ana bibiyar wadanda suka yi hulda da Ba'amurken da ya mutu a Ekiti

Covid-19 Hakkin mallakar hoto Getty Images

Gwamnatin Ekiti da ke Kudu maso yammacin Najeriya ta yi karin haske kan wani mutum dan asalin jihar da ya kamu da coronavirus, bayan ya tuka wani Ba'amurke.

Kwamishinar lafiyar jihar, Dr. Mojisola Yaya-Kolade cikin wata sanarwa ta ce ana zargin Ba'amurken da ya je daga jihar Virginia tare da rakiyar wata 'yar asalin jihar Ekiti, shi ne ya harbi mutumin dan shekara 38 da cutar COVID-19 bayan saukarsa a Najeriya.

Sanarwar ta ce Ba'amurken da 'yar rakiyarsa sun zo Najeriya ne ranar 3 ga watan Maris inda suka sauka a filin saman Murtala Mohammed da ke Lagos.

Ta ce binciken farko-farko ya nuna cewa dan Najeriyan da ya kamu da cutar coronavirus shi ne ya dauki Ba'amurken da 'yar rakiyarsa a mota ya tuka zuwa Ibadan, wurin da suka shafe tsawon kwanaki kafin su isa Ado Ekiti ranar 13 ga wata.

"Kwana guda kuma bayan isarsu ne sai Ba'amurken ya kamu da rashin lafiya, kuma aka dauke shi zuwa wani asibitin kudi, kafin a mayar da shi babban asibitin koyarwa, inda a can ne ya mutu," in ji sanarwar.

Ta ce hukumomin asibitin sun ankarar da kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da coronavirus na jihar Ekiti inda aka dauki samfurin jinin Ba'amurken tare da abokan tafiyarsa biyu.

Ta kara da cewa "gwajin da aka yi wa direban da ya kai su, ya nuna cewa cutar Covid-19 ta harbe shi, yayin da gwaji ya nuna ita 'yar rakiyar Ba'amurken ba ta dauke da cutar, shi kuma gwajin da aka yi wa mamacin a wannan lokaci bai kammala ba."

Bin sawu

Dr. Mojisola Yaya-Kolade ta ce bisa tanadin tsare-tsaren cibiyar takaita yaduwar cutuka ta Najeriya, tuni kwamitin kar-ta-kwanan da aka kafa ya kebe mutumin da ya kamu a wata kadaitacciyar cibiya.

"Ita kuma mai rakiyar Ba'amurken ana ci gaba da sanya ido kanta a wani wuri da ta kebe kanta," kamar yadda sanarwar ta shaida.

Kwamishinar lafiyar ta ce sun kuma fara bin sawun mutanen da suka yi hulda da su, inda suke aiki da ma'aikatar lafiya ta tarayya da Hukumar Lafiya ta Duniya ta hanyar bin diddigin wuraren da mutanen uku suka ziyarta bayan saukarsu a Najeriya.

Ta ce sun kuma tuntubi gwamnatin jihar Oyo tun da an fahimci cewa can ne mutanen suka ziyarta har suka shafe tsawon kwanaki kafin su isa jihar Ekiti.

A cewarta mutumin da aka tabbatar yana dauke da cutar COVID19 din yana nan cikin hayyacinsa, yayin da cibiyar takaita yaduwar cutuka za ta sake yi wa matar da suka zo da Ba'amurken gwaji.

Haka zalika, sanarwar ba ta yi karin haske kan halin da ake ciki game da Ba'amurken da gwamnatin jihar ta Ekiti ta ce gwajin farko da aka yi wa gawarsa, bai kammala ba.

A ranar Laraba ne hukumar dakile bazuwar cutuka a kasar ta sanar da samun karin mutum biyar masu coronavirus a Najeriya kuma kawo yanzu mutum takwas ne aka tabbatar suna dauke da cutar a Najeriya.

Karin labarai masu alaka da za ku so ku karanta

Labarai masu alaka