Coronavirus: Mece ce ita da kuma asalinta?

@ Hakkin mallakar hoto Getty Images

Annobar coronavirus ta kashe dubban mutane a fadin duniya, tun bayan bullar bakuwar cutar mai shafar numfashi a watan Disamban da ya gabata a kasar China.

Bakuwar cutar wadda aka fi sani da coronavirus ta yadu zuwa kasashe fiye da 150, abin da ya sa hukumomi daukar matakan hana yaduwarta da suka hada da killace garuruwan da aka samu bullarta, da makarantu da cibiyoyin kasuwanci da tarukan da kuma hana shigowar baki daga wuraren da aka samu bullar cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO na ambatar bakuwar cutar da suna COVID-19.

Wani kwararre a fannin lafiya kuma tsohon ma'aikacin Hukumar Lafiya ta Duniya Nasir Sani Gwarzo, ya yi wa BBC bayani game da asalin cutar da yanayinta da yadda take yaduwa da kuma matakan kariya.

Asalin coronavirus

A bayaninsa game da asalin cutar, da dalilin da ya sa ake kiranta coronavirus, wanda ya ce ba shi ba ne asalin sunanta ba ya ce:

"Shi coronavirus ba shi ne asalin sunan kwayar cutar ba, suna ne na danginta. Cutukan virus na da dangi biyu: masu sanda daya da masu sanda biyu.

"Masu sanda dayan (RNA) kuma sun kasu kusan kashi 17, to a cikin danginsu akwai dangin corona (coroavaride), shi ya sa ake kiran ta sabuwar kwayar cutar corona (Novel Coronavirus).

Masanin ya ce dalilin da ya sa ba a ayyana wa bakuwar cutar suna ba shi ne saboda ba a taba samun irin ta ba tarihi, sai wannan karon.

Yanayin cutar

Alamun cutar na kamanceceniya da na mura mai tsanani domin a cewarsa, "Tana sa tari da ciwon kai da zubar majina da ciwon makogoro da sauransu."

Sai dai ya yi karin haske game da bambancin ta da mura inda ya bayyana wa BBC yadda cutar ta bambanta da mura.

"Ta fi mura tsanani tun da tana haddasa zazzabi mai tsananin gaske kuma tana iya yin kisa."

Ya ce a cikin kowane mutum 200 da suka kamu da ita, za ta iya kashe mutum daya ko kasa da haka.

"Wannan shi ya sa ake damuwa a kanta, in ji shi."

Yadda cutar ke yaduwa

Cuta ce mai saurin yaduwa fiye da yadda ake zato, in ji shi. "Ana ganin idan mutum daya ya kamu, a cikin yini guda zai iya shafa wa mutum uku zuwa tara.

"Sannan a cikin kwana shida adadin zai iya ninkawa wajen hawa tara a cikin kankanin lokaci.''

Ya kara da cewa, "Misali idan mutum yana cikin taro, sai ya yi atishawa ko ya yi kaki ya tofar ko kuma ya face majina da hannunsa to zai iya shasshafa wa mutane a hannayensu."

Matakan kariya

Game da matakan kariya daga cutar, masanin lafiyar ya ce kula da matakan tsafta za su taimaka kwarai, duk da yake cutar bakuwa ce ba a gano kanta ba ko samo riga-kafinta.

Ya shawarci wadanda suke mura su daina shiga cikin taron jama'a ko kuma a ba su hutu har su samu sauki.

Sannan a bar tagogi a bude yadda iska za ta rika wucewa, musamman idan mai muran ba shi kadai ba ne a gidan.

Sauran shawarwarin da ya bayar su ne "kar a yi kaki da majina ko a sa majina a hannu a gaggaisa da mutane.

Sannan a rika yawan wanke hannu ko goga man tsaftace hannu (hand sanitizer). A guji yawan taba abubuwa a wurare, a yi kaffa-kaffa da hannu.

"Domin duk wanda yake yawan masabaha da mutane ko taba masu mura, nan da nan zai iya shafa wa fuskarsa kuma ya dauka.''