Tedros Adhanom Ghebreyesus: Mutumin da ke jagorantar yaki da cutar coronavirus

Composite of images of Dr Tedros Hakkin mallakar hoto AFP

Wane kalubale ne ga mutum ya kasance jagoran hukumar lafiya ta duniya a lokacin da ake fama da matsalar cutar 'Coronavirus'?

Duk fadin duniya an dogara ne da abin da za ka ambata, wato jawabi ga taron manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Geneva don yin cikakken bayani kan ci gaba da karuwar yawan mutanen da ke dada kamuwa da cutar a inda ake samun karuwar kasashen duniya da cutar ke kara bulla.

Wannan batun dan kasar Habashar nan kenan, Tedros Adhanom Ghebreyesus, dan Afirka na farko wanda ke shugabantar WHO, wanda ya kama aiki shekaru biyu da rabi da suka gabata.

Ya yi alkawarin aiwatar da sauye-sauye a hukumar, ya kuma shawo kan matsalar cututtukan da kan kashe miliyoyin mutane a duk shekara, irin su zazzabin cizon, cutar namoniya da kan kama yara kanana, da kwayoyin HIV mai karya garkuwar jiki.

Sai dai kuma yayin da WHO ke aiki tukuru kan yaki da wadannan cututtuka, mafi rinjayen zamanin shugabancin na Dokta Tedros da farko ya gamu ne da matsalar bullar Ebola a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo, a yanzu kuma ga cutar Covid-19.

Dukkan wadannan cututtuka biyu kuwa an ayyana su a matsayin wata matsalar lafiyar jama'ar da ke bukatar taimakon gaggawa, da kasashen duniya ke bayyana damuwa cikin gaggawa a kai.

'Mai kwarjini da saukin kai'

Wannan na nufin kenan suna bukatar sa ido a duk tsawon sa'o'i 24, tura ma'aikatan kiwon lafiya da kayan aiki da magunguna, da kuma tattaunawar yau da kullum da kasashen da abin ya shafa.

Da kuma tabbacin hakika na samar da sahihan bayanai ga kasashen duniya da suka kagauta su sami da ke matukar bukatar amsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A 2017 ne, Dr Tedros ya zama dan Afirka na farko da ya jagoranci hukumar WHO

''Mai kwarjini'' da ''saukin kai'' su ne kalmomin da wadanda suka san shi suke amfani da su wajen kwatanta wannan mutum mai shekara 55.

A wajen taronsa na farko na manema labarai a matsayinsa na babban daraktan WHO, ya rudar da 'yan jaridar da ke aiki a Geneva da yanayin halayyarsa.

Ya yi murmushi, ya zauna a tsanake, ya tattauna da murya mai sauki, har ma da kyar ake iya jin abin da yake fada sosai.

Wannan wani babban sauyi ne daga halayyar wadda ya gada mai tsare-gida, Margret Chan. Amma kuma a cikin irin wannan halayya ta saukin kai, akwai jajircewa.

Kafin ya zama shugaban WHO, ya sami daukaka a matakai daban-daban na gwamnatin kasar Habasha, har ya zama ministan lafiya, daga nan kuma ya zama ministan harkokin waje.

Da ya kasance nai dararewa, da bai kai matsayin da ya kai yanzu ba.

Kaninsa ya mutu a sakamakon cutar da ake zargin kyanda ce

An haifi Dokta Tredros a shekarar 1965 a garin Asmara, wanda ya zama babban birnin Eritrea bayan ta sami 'yanci daga kasar Habasa a shekarar 1991, ya kuma girma a yankin Tigray na arewacin Habashar.

Wani abu da ya taimaka wajen gina halayyarsa, a yanzu kuma ya zama abin karfafa gwiwa, shi ne mutuwar kanensa, yana dan kimanin shekara hudu da haihuwa a lokacin, kamar yadda ya shaida wa mujallar Time ta watan Nuwamba.

Daga baya kuma a matsayinsa na dalibi, Dokta Tedros ya yi zargin mai yiwuwa cutar kyanda ce ta halaka dan uwan nasa.

''Ban yarda da hakan ba, har yanzu kuma ban amince da hakan ba'', an ruwaito shi yana cewa, rashin adalci ne yaro ya mutu a sanadin cutar da za a iya magancewa, saboda kawai an haife shi a wani wuri da bai kamata .

''Dukkan hanyoyi sun nufi alkiblar samar da matakan kiwon lafiya ga kowa da kowa. Ba zan huta ba, har sai mun cim ma wannan manufa,'' ya kuma bayyana shaida wa babban taron WHO jim kadan kafin zaben sa a matsayin shugaban hukumar.

Dokta Tedros ya zama daya daga cikin 'yan kungiyar fafutukar kwatar 'yancin al'ummar yankin Tigray, wato ''Tigray People's Liberation Front'', wadda ke kan gaba wajen hambarar da mai mulkin kama karyar nan mai ra'ayin Makisanci, Mengistu Haile Mariam a shekarar 1991.

A matsayinsa na minista daga shekara ta 2005, ana gani ya fi saukin kusanta, da haba-haba fiye da wasu daga wasu abokan gwagwarmayarsa a kungiyar Tigray People's Liberation Front (TPLF).

An yaba masa kan sauyin da ya yi a bangaren kiwon lafiya a Habasha, wadda ke da yawa jama'a mafi girma a nahiyar Afirka, bayan Najeriya.

Amma yayin da yake kan aiki, ma'aikatarsa ta yi fice wajen karya wa 'yan jarida kwarin gwiwar bayar da labaran bullar cutar kwalara a kasar.

'Lallashin kasar Sin'

A lokacin da ya jagoranci wani gangamin hukumar lafiya ta duniya, wanda ya yi gagarumin tasiri, a karshe kuma ya sami nasara, magoya bayan Dokta Tedros sun yi watsi da zarge-zargen da ake yi cewa, ya yi rufa-rufa a lokutan barkewar cutar kwalara.

Yana da sanayya cewa, samun nasarar hukumar lafiya ta duniya wajen shawo kan matsalolin lafiya na duniya ta danganta ne ga hadin kan kasashe 194 da ke cikin kungiyar.

A lokacin matsalar da ake fama da ita a halin yanzu ta barkewar cutar Ebola a jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo, ziyarci kasar har sau uku, ba wai don kawai ya ga halin da ake ciki kadai ba, har don ya zanta da shugabannin gwamnati.

Daga nan ya yi saurin ziyartar kasar Sin yayin da aka sami labarin barkewar cutar coronavirus.

''Salon da ya bi na lallashin kasar Sin ta bi hanyar fayyace gaskiya, da samun hadin kan kasashen duniya, maimakon a yi ta sukar gwamnanti'', a cewar Lawrence Gostin, wani farfesa a fannin dokokin kiwon lafiya da ke Jami'ar Georgetown.

To, amma hakan ya yi aiki?

Wasu masu lura da harkokin WHO sun soki irin wanka da ruwan yabon da ake ta yi wa kasar Sin game da matakan kare cutar daga yaduwa.

Bayan ya ziyarci kasar ta Sin, Dokta Tedros y ace kasar ta shirya ''wani sabon daidaitaccen tsari na shawo kan barkewar cutar''.

Bayan 'yan kwanaki kadan kuma, ya shaida wa taron shugabannin kasashen duniya a Munich, cewa matakan da kasar Sin ta dauka sun ''sama wa kasashen duniya lokacin daukar matakan kandagarki''.

Wadannan bayanai suna fitowa ne kuwa, duk da rashin jin dadin kamun da kasar ta Sin din ta yi wa ma'aikatan lafiyar da suka fara kwarmata batun barkewar cutar.

Akwai kuma sukar da ake yi cewa, Dokta Tedros ya yi jinkiri ainun kafin ya bayar da sanarwar matakin gaggawa kan damuwar kasashen duniya game da kiwon lafiyar al'umma.

''Ina daya daga cikin wadanda suka fara ce masa ya bayar da sanarwar matakin gaggawar, a cewar Farfesa Gostin.

''Ko da na ambata hakan, dan jinkiri kadan aka samu, kuma ba na jin lokacin da aka yi sanarwar yana da wata illa ga tsarin da aka yi kan Covid-19."

''Sai dai kuma na dan damu, cewa wanka da ruwan yabo da ya yi wa kasar Sin, nan gaba zai iya rage kimar WHO, a matsayinta na wata hukumar kimiyya da aka amince da ita, wadda a ko yaushe a shirye take wajen fadar gaskiya ga masu mulki''.

Don haka, yayin da Dokta Tedros zai iya kasancewa da manufar siyasa, kokarin da aka yi ta fuskar siyasa ana ganin zai kare ne wajen sake tabbatar da mulkin kama karya, da gwamnatocin da ba sa kwatanta gaskiya, a kokarin jawo su domin su yi aiki tare da WHO, don shawo kan matsalar cututtukan da ke barazana ga lafiyar jama'ar duniya.

Hakkin mallakar hoto AFP

Idan ana maganar yadda gwamnatocin kasashen yamma da ke bin tsarin dimokradiya suke fahimtar wancan kokari, to mai yiwuwa dabarunsaba za su kasance kwarara matuka ba.

Ba da dadewa ba, bayan ya kama aiki, ya ba da shawara cewa, Robert Mugabe, shugaban kasar Zimbbwe a lokacin, ya zama jakadan WHO na nuna kauna.

Yana nuni cewa ya yi kokari wajen ganin Zimbabwe ta zama wata kasa ta mayar da ayyukan kiwon lafiyar al'umma da daukaka batun lafiya su zama kan gaba a manufofin siyasar kasar''.

Sai bayan da aka kwashe kwanaki ana nuna rashin amincewa, ba kawai daga gwamnatoci ba, amma daga kungiyoyin kare hakkin bil'Adama, wadanda suka yi tsokaci game da irin yadda gwamnatin Mugabe ta jefa mutanen kasar cikin wahala, sannan Dokta Tredos ya janye shawararsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dr Tedros ya kai ziyara kasar China gabanin ayyana cutar Coronavirus a matsayin annoba ta duniya

Karancin samar da kudi ga WHO

A yanzu, yayin da ake fama da barkewar wata sabuwar kwayar cuta a kasashen duniya, ana tababar da shawarwarinsa kuma.

Wasu sun bukaci ya ayyana cutar a matsayin annoba, wasu kuwa, ciki har da manyan jami'an WHO, sun nuna cewa, hakan magana ce kawai ta fatar baki, kuma ayyanawar ba za ta sauya dabarar WHO wajen shawo kan matsalar cutar ba.

Akwai kuma manazarta kwayoyin cuta da masu nazarin yaduwar cututtuka da shawo kansu, wadanda wasu daga cikinsu sun ce, shawarar da WHO ta ba kasashen da ke cikin kungiyar, cewa su yi amfani da kwararan matakai masu kaushi don magance cutar, wata shawara ce mai rauni.

Yayin da wasu ke ganin WHO ta yi zarbabi a martaninta.

Mun taba fuskantar irin wannan matsala a baya.

An soki Dokta Chan kana bin da ake hangen ta yi zarbabi a matakinta game da barkewar cutar murar aladu a shekara ta 2010, inda ta ayyana cutar a matsayin annoba, kuma ta ba kasashe shawarar su kashe miliyoyin kudi kan magunguna, abin da a karshe mafi yawa ba su yi ba.

Kana sai aka kuma ga ta yi matukar jan kafa wajen daukar mataki kan masifar nan ta cutar Ebola da ta barke a yankin yammacin Afirka, wadda ta lakume rauyka mutane dubu goma sha daya.

''Tir idan ka yi, tir idan ba ka yi ba'', wadannan kalaman ne za ka yawaita jin ana ambatawa a hedikwatar WHO.

Farfesa Gostin ya yi amanna cewa, Dokta Tedros ya zama wata alama ta shugabanci a lokacin matsalar cutar 'coronavirus'.

Amma kuma, ya yi gargadi cewa har yanzu muhimman matsalolin rauni da hukumar lafiya ta duniya suna nan, ciki kuwa har da karancin samun kudi.

Sai gobe

Ba za a iya tantance nasarar Dokta Tedros, da ma hukumar lafiya ta duniya baki daya, game da magance cutar 'coronavirus' ba, har sai an kai ga karshen matsalar.

A yanzu kam, zai ci gaba ne da ba kasashe shawara su shirya, su gano cutar, a gudanar da bincike, kuma a kula da matsalar.

A duk rana yakan yi jawabi ga manema labarai, a kullum ana yayata kalamansa a sassan duniya.

Kuma duk da matsin lambar da ake yi masa a kan ya fito da amsoshi, duk da yadda kafofin yada labarai kan mayar da hankali kansa, ya ci gaba da kasancewa cikin natsuwa tare da haba-haba.

Karshen kowanne taron manema labarai a ko yaushe yakan kasance iri daya; tarin takardu, murmushi, da kuma cewa ''sai gobe''.