Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon nan: 6-12 March 2020

Mahaya dawakai sun halarci jana'iza ranar Lahadi a wurin da aka samu hadarin jirgin Ethiopia kirar 737 Max.... Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mahaya dawakai sun halarci jana'iza ranar Lahadi a wurin da aka samu hadarin jirgin Ethiopia kirar 737 Max....
An gudanar da wani taron bayan kwana biyu don tunawa da ranar da jirgin ya yi hadari. Jirgin da ke kan hanyar zuwa Kenya ya yi hadari ne jim kadan bayan ya tashi daga Addis Ababa, babban birnin Ethiopia. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An gudanar da wani taron bayan kwana biyu don tunawa da ranar da jirgin ya yi hadari. Jirgin da ke kan hanyar zuwa Kenya ya yi hadari ne jim kadan bayan ya tashi daga Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.
Wasu maza na tsaftace makabarta a Monrovia babban birnin Liberia ranar Laraba - ranar hutu da ake kira ranar yin gyara inda mutane suke gyara makabartun 'yan uwansu. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wasu maza na tsaftace makabarta a Monrovia babban birnin Liberia ranar Laraba - ranar hutu da ake kira ranar yin gyara inda mutane suke gyara makabartun 'yan uwansu.
Ana rakiyar shugabannin hamayya a Tanzania zuwa kurkuku bayan sun halarci zaman kotu a Dar ed Salaam ranar Talata bayan an nemi su biya tarar $150,000 saboda gudanar da taro ba bisa ka'ida ba. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana rakiyar shugabannin hamayya a Tanzania zuwa kurkuku bayan sun halarci zaman kotu a Dar ed Salaam ranar Talata bayan an nemi su biya tarar $150,000 saboda gudanar da taro ba bisa ka'ida ba.
Wani yaro kenan da yake fareti ranar Juma'a yayin da ake bikin zagayowar ranar da Ghana ta samu 'yancin kai a birnin Kumasi. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani yaro kenan da yake fareti ranar Juma'a yayin da ake bikin zagayowar ranar da Ghana ta samu 'yancin kai a birnin Kumasi.
Wasu masu rawa da suma suka halarci bikin cikar Ghana shekara 63 da samun 'yancin kai Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wasu masu rawa da suma suka halarci bikin cikar Ghana shekara 63 da samun 'yancin kai
A dai ranar, wani mutum kenan sanye da takunkumin fuska a wajen kofar shiga babban asibitin Yaounde a Kamaru - inda ake kula da dan kasar Faransa da ya kamu da cutar Covid-19. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A dai ranar, wani mutum kenan sanye da takunkumin fuska a wajen kofar shiga babban asibitin Yaounde a Kamaru - inda ake kula da dan kasar Faransa da ya kamu da cutar Covid-19.
A ranar Litinin wasu masu zanga-zanga kan rikicin da ake a yankunan Ingilishi sun taru a London da ke Burtaniya. Hakkin mallakar hoto PA Media
Image caption A ranar Litinin wasu masu zanga-zanga kan rikicin da ake a yankunan Ingilishi sun taru a London da ke Burtaniya.
Mata a Algeria sun yi tattaki a Algiers babban birnin kasar domin bikin ranar mata ta duniya da aka yi ranar Lahadi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mata a Algeria sun yi tattaki a Algiers babban birnin kasar domin bikin ranar mata ta duniya da aka yi ranar Lahadi
A dai ranar bikin matan kuma a Khartoum da ke Sudan, hoton wata mata ne ya bazu inda ta daga hannunta dauke da zane yayin wata zanga-zangar neman soke dokar iyali ta kasar wadda masu zanga-zangar suka ce ta na nuna wariya ga mata. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A dai ranar bikin matan kuma a Khartoum da ke Sudan, hoton wata mata ne ya bazu inda ta daga hannunta dauke da zane yayin wata zanga-zangar neman soke dokar iyali ta kasar wadda masu zanga-zangar suka ce ta na nuna wariya ga mata.
Wani maciji ya kanannade wata mata a birnin Johannersburg da ke Afirka ta Kudu ranar Asabar Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani maciji ya kanannade wata mata a birnin Johannersburg da ke Afirka ta Kudu ranar Asabar
Hoton wani mai tseren keke ne yake zagaye yankin Masiphumelele a kusa da Cape Town..... Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hoton wani mai tseren keke ne yake zagaye yankin Masiphumelele a kusa da Cape Town.....
Masu tseren keke na fafatawa a gasar tseren keke mafi girma a duniya a birnin Cape Town. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masu tseren keke na fafatawa a gasar tseren keke mafi girma a duniya a birnin Cape Town.
Wasu yara kenan da ke wasa a bikin Holi - wani biki da mabiya addinin Hindu ke gudanarwa domin murnar sabuwar rayuwa... Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu yara kenan da ke wasa a bikin Holi - wani biki da mabiya addinin Hindu ke gudanarwa domin murnar sabuwar rayuwa...
Ana yi wa bikin taken "bikin kaloli"… Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana yi wa bikin taken "bikin kaloli"…
Kuma ana watsa hoda da ruwa mai kala Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kuma ana watsa hoda da ruwa mai kala
Firai Ministan Lesotho da ya ce ba za a iya tuhumarsa da kisan matarsa ba saboda matsayinsa ya ba shi kariya daga tuhuma, ya halarci wani gangami ranar Lahadi. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firai Ministan Lesotho da ya ce ba za a iya tuhumarsa da kisan matarsa ba saboda matsayinsa ya ba shi kariya daga tuhuma, ya halarci wani gangami ranar Lahadi.
Ranar Talata, Ahlem Souidi ta bayyana kan mumbari a Tunis kafin a bayyana ta a matsayin wadda ta fi kowa kyau a Larabawa Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ranar Talata, Ahlem Souidi ta bayyana kan mumbari a Tunis kafin a bayyana ta a matsayin wadda ta fi kowa kyau a Larabawa
Nan kuma wasu masu nuna al'adar gargajiya ce daga Mali inda suke baje ta su al'adar a birnin Abidjan da ke Ivory Coast. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nan kuma wasu masu nuna al'adar gargajiya ce daga Mali inda suke baje ta su al'adar a birnin Abidjan da ke Ivory Coast.
Ma'aikata na tsaka da aiki a tashar jirgin saman Abuja babban birnin Najeriya ranar Alhamis. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ma'aikata na tsaka da aiki a tashar jirgin saman Abuja babban birnin Najeriya ranar Alhamis.
Wata yarinya na wanke hannayenta ranar Laraba a daya daga cikin famfunan da aka samar a tashoshin mota a Kigali babban birnin Rwanda a yunkurin magance bazuwar Covid-19. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata yarinya na wanke hannayenta ranar Laraba a daya daga cikin famfunan da aka samar a tashoshin mota a Kigali babban birnin Rwanda a yunkurin magance bazuwar Covid-19.
Cutar coronavirus ta bude wa wani mai sayar da kaya a bakin titi a Johannesburg damar kasuwanci inda yake sayar da man tsaftace hannu ga masu tuka mota. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cutar coronavirus ta bude wa wani mai sayar da kaya a bakin titi a Johannesburg damar kasuwanci inda yake sayar da man tsaftace hannu ga masu tuka mota.

Hotuna daga AFP, EPA, PA and Reuters

Labarai masu alaka