Wanne tasiri rikicin APC zai iya yi a kan jamiyyar?

Shugabannin jam'iyyar APC Hakkin mallakar hoto @OfficialAPCNg

A bayyane take cewa rikicin da ke ruruwa a APC mai mulkin Najeriya ya taso ne a kokawar da wasu 'yan jam'iyyar suke yi na tabbatar da ikonsu gabanin zaben 2023.

Zaben na 2023 ne zai tabbatar ko Kuma ya kore ikirarin da wasu masu nazari kan harkokin siyasa suka yi cewa APC ba jam'iyya ba ce, illa dai kawai wata gamayyar 'yan siyasa ne masu mabambantan ra'ayoyi da suka hadu domin kawar da jam'iyyar PDP daga mulki a 2015.

Rikicin baya bayan nan shi ne game da hukuncin wata kotun Abuja wadda ta tabbatar da sauke Mr Adams Oshimhole daga shugabancin jam'iyyar.

Mai Shari'a Danlami Senchi ne na kotun ta Abuja ya yanke hukuncin bayan karar da wani dan jam'iyyar APC, Oluwale Afolabi, ya shigar cewa tuni aka dakatar da Mr Oshiomhole daga jam'iyyar APC a jiharsa ta Edo.

Mai Shari'a Senchi ya kuma haramta wa Mr Oshiomhole shiga hedikwatar jam'iyyar. Daga bisani an jibge jami'an 'yan sanda a kofar shiga hedikwatar jam'iyyar.

Da alama wannan hukunci ya tayar wa Mr Oshiomhole hankali inda ya garzaya fadar shugaban kasa domin ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari.

Kuma kamar yadda aka zata, ya shaida wa manema labaran fadar shugaban kasar cewa wasu gwamnoni ne na APC da kuma wasu manyan 'yan jam'iyyar suke son cire shi daga kan mukaminsa.

Watakila za a iya cewa kalaman na shugaban APC da ke cikin rigima na da kanshin gaskiya ganin cewa sakatariyar gwamnonin APC ta bakin kakakinta Abdurrahman Barkindo ta fitar da sanarwar da ke goyon bayan hukuncin kotun.

Sai dai a wani mataki da ake gani na samun goyon bayan gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ne, wata kotun tarayya da ke jihar ta Kano ta yi fatali da hukuncin kotun Abuja, inda ta jaddada cewa Mr Oshiomhole shi ne halastaccen shugaban APC.

Amma kamar yadda masana siyasa ke cewa, masu yunkurin kawar da Mr Oshiomhole sun riga sun ja daga. Wani bangare da ke kiran kansa reshen APC da ke kudu maso kudancin Najeriya, wanda fitattun 'yan siaysar yankin irin su gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da tsohon gwamnan Ribas kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi ke cikin sa, ya nada Mr Victor Giadom a matsayin shugaban riko na jam'iyyar.

An dade ana kai ruwa rana tsakanin Mr Obaseki, wanda shi ne mutumin da ya maye gurbin Mr Oshiomhole a matsayin gwamnan Edo da tsohon mai gidan nasa, lamarin da wasu ke gani shi ne silar sabon rikicin da ke kokarin cin kujerar Mr Oshiomhole.

Watakila wannan sa-toka-sa-katsi ne ya sa daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu, ya fusata inda a wata wasika da ya rubuta a karshen makon jiya, ya yi zargin cewa zazzabin cutar samun mulki a 2023 ne ya kama mutanen da ke yunkurin cire Mr Oshiomhole daga shugabancin APC.

Mr Tinubu ya ce ya zama wajibi 'yan jam'iyyar su hada hannu "domin kawar da duk wata cuta" a cikin jam'iyyar.

"Wata dadaddiyar cuta ce ta bukatar 2023, wadda ta damu wasu 'yan siyasa da kuma abokansu 'yan jarida," in ji Tinubu.

Masana harkokin siyasa, irin su Dr Abubakar Kyari na Jami'ar Abuja da ke Najeriya, sun ce rikicin APC zai iya yi mata illa sosai idan ba a shawo kansa ba. Ya ce rikicin da wuya kuma a shawo kansa ganin cewa kowa da inda ya sa gaba a jam'iyyar.

Dr Kari ya shaida wa BBC cewa "Muna fada muna nanatawa cewa har yanzu APC ba ta zama cikakkiyar jam'iyya ba, gungu-gungu ne na mutane da ke da akidu daban-daban wadanda a baya ma fada suke yi da juna," in ji Dakta Abubakar Umar Kari, masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja.

Ya kara da cewa abin da kawai ya hada 'yan jam'iyyar APC shi ne "wata dama da za su karbi mulki a shekarar 2015".

Wasu masana siyasa na ganin cewa rikicin APC ya soma ne tun lokacin tsayar da 'yan takara a zaben 2019 inda wasu 'yan jam'iyyar da ma mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari suka yi zargin cewa shugabanta Mr Oshiomhole ya yi rashin adalci ga wasu masu neman yi wa jam'iyyar takara na mukaman gwamnoni da 'yan majalisu.

A cewarsu, barinsa ya ci gaba da shugabancin jam'iyyar zai iya durkusar da ita, ko da yake Mr Oshiomhole ya sha musanta hakan yana mai cewa halayyarsa ta kin bari a rika juya shi kamar yadda wasu 'yan jam'iyyar suke so ne ta sa suke son cire shi daga mulki.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Presidency
Image caption Adams Oshiomhole (hannun hagu) ya garzaya wurin Shugaba Buhari jim kadan bayan wata kotu ta sauke shi daga kan mukaminsa, ko da yake wata kotun ta janye hukuncin

Wani batu kuma shi ne yadda wani bangare da ke adawa da Mr Oshimohle ya bukaci a gudanar da taron kwamitin zartarwar jam'iyyar wanda ake gani ana son yin sa ne domin yin amfani da shi wurin cire shugaban jam'iyyar.

Ko da yake taron da wasu gwamnonin jam'iyyar suka yi da Shugaba Buhari ranar Litinin, ya dakatar da gudanar da taron kwamitin zartarwar, wasu masana harkokin siyasa na ganin rikicin siyasar da yake ci gaba da ci a APC zai koma na saki-ka-noke ne kawai kuma nan gaba zai sake bullowa.

Amma wasu masu nazari na gani taron koli na jam'iyyar ta APC da aka gudanar ranar Talata, inda shugabanta ya jagoranci yi wa wasu manyan jami'an jam'iyyar, wato mataimakin shugaban jam'iyar a yankin arewa maso yamma Senata Lawal Shu'aibu da kuma mataimakinsa Abdulkadir Inuwa afuwa bayan dakatar da su da aka yi tsawon wata shida, zai iya zama wata hanya ta dinke barakar jam'iyyar.

Labarai masu alaka