Najeriya ta hana shigowa daga kasashe 13 kan coronavirus

corona Hakkin mallakar hoto Getty Images

Najeriya ta hana baki shigowa daga China da Italy da Amurka da Birtaniya da Iran da ma wasu kasashen da coronavirus ta yi kamari.

Hukumar hana kare yaduwar cututtuka ta kasar ce ta sanar da hakan a ranar Laraba a shafinta Twitter.

Sauran kasashen da Najeriyar ta hana baki shiga cikinta sun hada Koriya Ta Kudu da Spaniya da Faransa da Jamus da Norway da Netherlands da kuma Switzerland.

NCDC ta ce akwai masu dauke da cutar fiye da 1,000 a kowacce daga cikin kasashen nan.

Haka kuma, Hukumar ta sanar da cewa za a killace duka matifiya da za su iso kasar daga wadannan kasashen.

Sannan Najeriya za ta dakatar da ba da takardun shiga wato biza ga 'yan kasashen nan 13.

Wannan mataki na zuwa ne bayan da kasashen Afirka da dama suka dauki irin sa.

Ko a ranar Talata dai gwamnatin Najeriya ta ce rufe sararin samainyarta da hana baki shigowa ta jiragen sama ba abu ne da ya zama wajibi ba, amma hakan ya sa 'yan kasar sun yi wa gwamnati ca, musamman bayan da aka samu mutum ta uku da ta kamu da cutar a Legas.

Matar ta dawo ne daga Birtaniya ranar Juma'a 13 ga watan Maris, inda hukumomi a ranar Talatar suka tabbatar tana dauke da cutar, har ma ana neman wadanda suka zo a wannan jirgin na British Airways da su killace kawaunansu a inda suke.

Labarai masu alaka