An samu karin mutum biyar masu coronavirus a Najeriya

coronavirus Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana binciken lafiyar mutane a filayen jiragen sama na Najeriya

An samu karin mutum biyar masu coronavirus a Najeriya in ji hukumar da ke kare yaduwar cututtuka ta kasar.

Hukumar yaki da yaduwar cutuka a Najeriya ce ta tabbatar da hakan a ranar Laraba a shafinta na Twitter.

Hukumar ta ce duka masu dauke da cutar sun dawo ne daga Burtaniya ko Amurka kwanan nan.

A cewarta, a cikin mutanen har da wata mata da jaririyarta mai mako shida a duniya da kuma wani dan Amurka, wanda ya shiga kasar ta tsandauri, inda ya kasance mutum na farko da ya shigo da cutar ba ta jirgin sama ba.

Hukumar ta ce an tattara bayanai kan dukkan mutanen da zummar gano wadanda suka yi mu'amala da su.

Ta yi kira ga 'yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu yayin da jami'an kiwon lafiya ke daukar dukkan matakan da suka dace don yaki da yaduwar cutar a kasar.

Kawo yanzu mutum takwas ne aka tabbatar suna dauke da cutar a Najeriya.

Labarai masu alaka