Coronavirus: Za a rufe makarantu a jihohin arewa maso yamma

Gwamnonin arewa maso yamma Hakkin mallakar hoto Twitter/@elrufai

Gwamnonin jihohin arewa maso yammacin Najeriya sun ce za a rufe dukkan makarantu a jihohin saboda fargabar cutar coronavirus.

Gwamnonin sun dauki matakin ne ranar Laraba bayan taron da suka gudanar a birnin Kaduna.

Jihohin su ne Kano da Kaduna da Jigawa da Kebbi da Sokoto da Zamfara da kuma Katsina.

Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya shaida wa BBC cewa suna sa ran rufe makarantun ranar Litinin mai zuwa bayan sun tattauna da hukumar jarrabawar sakandare da takwararta ta share fagen shiga jami'a.

"Za mu tattauna da hukumomin ne domin su ba mu shawara kan yadda za a bullowa daliban da ke rubuta jarrabawar JAMB da kuma jarrabawar kammala sakandare wacce za a soma a watan Afrilu.

"Ba ma son rufe makarantun ta shafi dalibai shi ya sa muke son tattaunawa da wadannan hukumomi," a cewar Gwamna Badaru.

Ranar Laraba hukumomin lafiya a Najeriya suka ce an samu karin mutum biyar masu dauke da coronavirus a kasar.

Hakan na nufin yanzu mutum takwas ne aka tabbatar suna dauke da cutar a Najeriya.

Kazalika gwamnatin Katsina ta ce an samu wani mutum da ake zargi ya kamu da cutar, ko da yake yanzu ana can ana yi masa gwaji domin gano hakikanin abin da ya faru da shi

Hakkin mallakar hoto Twitter/@elrufai

Labarai masu alaka