Ali Nuhu ya yi magana kan cutar Coronavirus

Tauraron fina-finan Kannywood, Ali Nuhu, ya ce ya fada cikin fargaba lokacin da ya soma samun labarin bullar cutar coronavirus.

Ya bayyana wa BBC haka ne a wurin bikin bayar da lambar yabo ga taurarin fina-finai da aka gudanar a Lagos a karshen mako.

Sai dai tauraron ya ce yana da yakini za a samu maganin cutar.