Coronavirus ta rage wa Najeriya dogon burinta a 2020

REUTERS Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Najeriya tana daukar matakai a matsayin kandagarki don dakile tasirin coronavirus a kan tattalin arzikin kasar

Ministar kudin Najeriya ta ce gwamnatinsu ta ga bukatar tsayawa ta yi kididdiga kan tasirin annobar COVID-19 da kuma yadda faduwar farashin man fetur zai shafi tattalin arzikin kasar.

Dr Zainab Shamsuna yayin gabatar da jawabi ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwar kasar a ranar Laraba, ta ce matakin zai hadar da ayyukan da aka sanya cikin kasafin kudin 2020 da ma wadanda ba a sa a kasafin ba.

Ta ce manyan ayyukan da za a zaftare sun kai jimillar naira tirliyan 1.5 a cikin kasafin kudi.

Raguwar farashin danyen man fetur daga dala 57 a kan duk gangar man fetur da Najeriya ta tsara a kasafin kudin zuwa dala 30 na nufin cewa kudaden shigar da za ta samu za su ragu sosai da sosai.

"Kusan kashi 45 cikin 100, kasa da abin da muka tsara saboda haka akwai bukatar mu yi gyaran fuska kan dumbin hasashen da muka yi a kasafin kudi da kuma cikin tsarin kashe kudi na matsakaicin wa'adi don su dace da zahirin halin da ake ciki," a cewar Zainab Shamsuna.

Ta ce suna duba yiwuwar bunkasa adadin man fetur da ake hakowa don tabbatar da ganin a kalla Najeriya na samar da ganga miliyan 2.18 mafi karanci, kamar yadda aka tanada a cikin kasafin kudin 2020.

Hakkin mallakar hoto @FinMinNigeria

Jihohi na tsaka mai wuya

Ministar ta ce tabbas sun damu da halin da tattalin arzikin kasar yake ciki. Don kuwa tana iya samun raguwar kudin shiga da kimanin kashi 40 zuwa 45.

Kuma a cewar Zainab lamarin zai shafi jihohi saboda kudaden da ake rabawa a matakan gwamnatocin kasar uku zai yi matukar raguwa.

Don haka ta ce suna sa rai su ma jihohi za su dauki makamantan wadannan matakai don yi wa tsare-tsarensu na kudi garambawul ta yadda za su dace da halin da ake ciki.

"Muna aiki ne bisa hasashen cewa komai bacin rana, gangar man fetur ba za ta gaza dala 30 a kasuwa ba, kuma za mu tabbatar adadin gangar man da muke hakowa a kullum ya kasance a kalla miliyan 2.18, a cewar ministar.

Karin batutuwan da majalisar zartarwar ta tattauna kansu akwai dakatar da daukar ma'aikata, sai dai a bangarorin da suka zama tilas ciki har da tsaro da lafiya.

Bunkasa rayuwar al'umma

Dr. Zainab ta ce an kuma bukaci su yi bitar yadda ake aiwatar da shirin bunkasa rayuwar al'umma wato Social Investment Programme, da kuma daga kafar da bai zama tilas ba kan wasu haraje-haraje ta yadda gwamnati za ta samu karin kudaden shiga.

Daga cikin sauye-sauyen da za a yi wa kasafin kudin bana na Najeriyar har da rage yawan harajin da hukumar kwastam aka sa rai tun farko za ta samu a bana na naira tiriliyan 1.5.

Zainab ta ce an yi haka ne bisa tunanin cewa yawan hada-hadar kasuwanci zai ragu.

Haka zalika ta ce an amince da rage hasashen kudin da ake sa ran samu zuwa kashi 50 cikin dari daga ribar cefanar da kadarorin gwamnati.

Zaburar da tattalin arziki

A wani bangare kuma, Babban Bankin Najeriya ya sanar da daukar karin matakan zaburar da tattalin arzikin kasar yayin da cutar covid-19 ke kara ta'azzara a fadin duniya.

Kan haka ne ya ce zai zuba karin naira tiriliyan guda don zaburar da tattalin arzikin kasar.

Haka zalika, bankin ya kuma bayyana aniyar samar da wata naira biliyan 100 rance don bunkasa bangaren lafiya.

Ya kuma ce wani asusun naira tiriliyan daya da rabi na gudunmawar 'yan kasuwa wajen samar da ababen more rayuwa yana nan kan hanya, a karkashin kwamitin aiki kan tunkarar coronavirus don sada manoma da kasuwanni.

Haka kuma ya umarci bankunan kasuwanci su rubanya tallafin da suke samarwa don mara baya ga masana'antun harhada magunguna da cibiyoyin kula da lafiya.