Likitoci na zabar wanda zai rayu da wanda zai mutu saboda coronavirus

Doctors in Padova, northern Italy Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yankin arewacin Italiya ne coronavirus ta fi muni a can

Likitocin da ke gaba-gaba wajen yaki da coronavirus a Italiya sun ce suna fuskantar wani mummunann hali na zabar wanda zai rayu ta hanyar yi musu magani da wanda za su kyale ya mutu ga masu fama da cutar.

A yayin da ake samun karuwar daruruwan masu dauke da cutar a kowace rana, Italiya na ta kokarin samar da isassun gadajen asibiti da za su duba marasa lafiya.

Shugaban sashen kulawa ta musamman a asibitin Bergamo da ke yankin arewacin Lambordia, Dr Christian Salaroli, ya shaida wa jaridar Corriere della Sera cewa: "Idan mutum ya kai tsakanin shekara 80 zuwa 95 kuma yana cikin tsananin yanayi na cutar, to watakila ba za ka iya ci gaba da ba shi kulawa ba.''

"Akwai kalamai masu matukar tayar da hankali, amma kuma a zahiri su ne gaskiyar magana. Ba za mu iya yin abin da za ku kira mu'ujiza ba"

Amma mene ne tattare da wannan annoba a Italiya da har za ta sa a zabi rayuwar wasu a kyale ta wasu?

'Zabi mai wahala'

Coronavirus ta yi muni sosai a Italiya - an samu mace-mace har 1,000 daga cikin mutum 15,000 masu dauke da cutar a ranar Juma'ar da ta gabata, wato 12 ga watan Mairs 2020, kusan kashi uku na yawan mace-macen da aka samu a China.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yawan mace-mace ya kai 1,000 a Italiya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Italiya ce kasa ta biyu da ta fi yawan tsofaffi baya ga Japan a duniya, abin da ke nufin suna cikin hadarin shiga mummunan yanayi idan cutar ta kama su.

A farkon wannan watan ne, kungiyar likitocin da suka kware a yin allurar sa bacci lokacin tiyata ta saki wasu shawarwari ga likitoci, kan wa ya kamata su bai wa gado a asibiti tare da bai wa kulawa, abin da hakan ke nufin ba kowa ne zai samu gado ba.

Maimakon bayar da kulawa ga duk wanda aka fara kawo wa asibiti, kungiyar ta shawarci likitoci da malaman jinya da su dinga runtse ido su ba da kulawa ga mutanen da aka fi sa ran za su warke bayan yi musu magani.

Kungiyar ta ce: "Ba wai muna ba da shawarar a ki duba wasu ba ne. Halin da ake ciki ne yake tursasa likitocin su mayar da hankalinsu kan wadanda aka fi sa ran za su warke."

'Tsunami'

Akwai gadaje a bangaren kula ta musamman kusan 5,200 a Italiya, amma a watannin hunturu yawancin gadajen kan cika da marasa lafiya da ke fama da matsalar numfashi.

Akwai gadaje 1,800 kawai a yankunan Lombardy da Veneto a cibiyoyin lafiya na gwamnati da masu zaman kansu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Asibitocin yankin arewacin kasar na fama da rashin isassun gadon kwantar da marasa lafiya

Dr Stefano Magnone, wanda ke aiki a wani asibiti a Lombardy, ya shaida wa BBC cewa suna kure yawan kayan aikin da ke hannunsu.

"Lamarin na kara muni a kowace rana, saboda muna kure adadin yawan gadajen da muke da su a bangaren kulawa ta musamman da ma sauran bangarorin don yi wa masu dauke da coronavirus magani," a cewarsa.

"A yankinmu, ba mu da sauran wajen ajiye marasa lafiya, sannan duk kayan aikinmu sun kare, muna jira a kawo mana wasu."

A farkon makon nan wani sako da wani likira a asibitin Bergamo Dr Daniele Macchini ya wallafa a Twitter ya yadu kamar ruwan dare.

A ciki ya bayyana yadda tawagarsa take matukar fama da abin da ya kira ''tsunami'' ta yadda kayan aiki suka zama tamkar zinare don daraja.

"Masu dauke da cutar na karuwa, a kowace rana mu kan samu mutum 15 zuwa 20 da ake kwantar da su a asibiti.

"Yawanci sakamakon gwajin suna zuwa ne daf da daf, kowane na nuna marasa lafiyar na dauke da cutar. Sannan ga dakin ba da taimakin gaggawar yana durkushewa," in ji shi.

"Wasu daga cikin abokan aikinmu da suka kamu sun shafa wa 'yan uwansu, kuma tuni wasu daga cikin dangin nasu ke cikin halin mutu kwakwai rai kwakwai.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jami'an lafiya sun ce suna cikin wani irin yanayi

Dr Salaroli ta shaida wa jaridar Corriere cewa yanayin da ma'aikatan lafiya suke ciki ''na tashin hankali ne'' kuma wasu likitocin a tawagarsa suna shiga halin dimuwa kan zabin da suke da shi na su kula da mutum ko su bar shi ya mutu.

"Zai iya faruwa ga babban likita ma balle kuma matasan likitoci da kwanan nan suka fara aikin, suka samu kansu a yanayin da dole suna gani za su bar wasu su mutu.

"Na ga yadda malaman jinya da suka yi shekara 30 suna aiki ke kuka, saboda wannan yanayi."

'Rokon Italiya ga Turai'

Da yake magana da BBC, Minsitan Harkokin Wajen Italiya, Luigi Di Maio, ya yi kira ga a samar da cibiya daya a yankin Turai da za ta samar da kayayyakin da asibitoci ke bukata a yankin.

Amma ya bayyana jin dadi ga yadda har yanzu ba a samu bullar cutar ba a wasu garuruwa 10 da ke arewacin Italiya inda aka sanya dokar ta baci.

"Italiya ce kasa ta farko a Turai da lamarin ya fi muni," a cewar Di Maio. "Amma ina fatan hakan ya sa kasar ta zamo ta farko da za ta fice daga wannan mummunan yanayi."

Labarai masu alaka