Shin ibuprofen yana maganin coronavirus?

A woman holds a painkiller pill and a glass of water Hakkin mallakar hoto Getty Images

An yi ta watsa labarai a shafukan intanet da ke cewa shan maganin ibuprofen ga mutanen da ke fama da cutar coronavirus na da matukar hatsari.

A yayin da ake bayar da sahihan bayanan kiwon lafiya kan cutar, haka kuma ana ci gaba da watsa labaran karya a kanta.

Masana kiwon lafiya sun shaida wa BBC cewa ba su bayar da shawarar yin amfani da ibuprofen domin yin riga-kafin coronavirus ba.

Sai dai sun ce mutanen da ke shan ibuprofen domin maganin wasu cutukan za su iya ci gaba da yi idan ba likitoci ne suka hana su sha ba.

Kwayoyin maganin paracetamol da ibuprofen suna rage zafin jikin mutum da kuma warkar da mura.

Amma bai dace kowanne mutum ya sha ibuprofen da dangoginsa ba domin yana haifar da wata illar - musamman ga mutanen da ke fama da tarin asthma, ko ciwon zuciya.

A baya dai, hukumar lafiya ta Burtaniya ta wallafa a shafinta cewa babu laifi idan mutum ya yi amfani da paracetamol da ibuprofen.

Amma tun tuni ta sauya matsayinta inda ta ce "babu wata kwakkwarar hujja da ke nuna cewa shan kwayoyin ibuprofen zai iya ta'azzara coronavirus (Covid-19) ... don haka ku ci gaba da amfani da paracetamol domin shawo kan alamun cutar coronavirus, har sai likitoci sun gaya muku cewa bai kamata ku yi amfani da paracetamol ba."

Hukumar lafiya ta Burtaniya ta kara da cewa ka da mutanen da likitoci suka ba su shawarar shan ibuprofen su daina, har sai sun gaya musu su dakata.

Ko da yake har yanzu ba mu sani ba ko ibuprofen na da tasiri kan tsanani ko kuma girman cutar da kwayar cutar coronavirus ke haddasawa - a kan mutanen da ke da lafiya ko wadanda ke fama da rashinta.

Dr Charlotte Warren-Gash, ta the London School of Hygiene and Tropical Medicine, ta ce, mutanen da ke da yiwuwar kamuwa da cutar, "da alama zai yi kyau a gare su su rika shan paracetamol a matsayin zabinsu na farko".

Kazalika akwai wasu shaidu da ke alakanta ibuprofen da zazzabi mai zafi daga sauran cutukan da suka shafi numfashi.

Labaran karya

Amma kowacce shawara aka bayar game da amfani da ibuprofen, akwai labaran karya sosai da ake watsawa a kansa a shafukan intanet. Sakonnin karya da ake watsawa a WhatsApp sun hada da wadanda ke cewa:

? "An kwantar da matasa hudu a sashen bayar da agajin gaggawa na asibitin Cork wadanda ke fama da cutar - dukkan su suna shan maganin rage radadi kuma ana fargabar hakan zai haifar da cutuka masu zafi" (labarin karya)

? Jami'ar Vienna ta aike da sakon da ke gargadin mutanen da ke nuna alamun kamuwa da coronavirus kada su sha ibuprofen, "saboda an gano cewa yana kara hayayyafar da coronavirus Covid-19 ke yi a gangar jiki kuma wannan ne dalilin da ya sa aka samu ta'azzarar cutar a tsakanin 'yan kasar Italiya da ma yaduwar cutar sosai." (labarin karya)

? "A Jami'ar Toulouse da ke Faransa, akwai matasa hudu da ke fama da matsananciyar cutar coronavirus wadanda ba sa fama da wasu cutukan. Matsalarsu ita ce, lokacin da suka ji alamar kamuwa da coronavirus, sun rika shan magungunan rage radadi irin su." (labarin karya)

Wadannan labaran da ake watsawa a manhajar WhatsApp, ana kuma yada su a sauran shafukan sada zumunta ciki har da Instagram.

Galibi ana ikirarin cewa wani ne wanda mutanen da ke yada wadannan labaran suka sani ya turo musu domin su watsa.

Dukkan wadannan labaran karya ne

Kungiyar likitocin cutuka masu yaduwa ta Ireland ta ce sakonnin da ake watsawa a WhatsApp kan masu fama da coronavirus a Cork "karya" ne, inda ta yi kira ga duk wanda ya samu sakon ya yi watsi da shi.

Asibitin Jami'ar Toulouse ya yi gargadin cewa labaran karya kan cutar na bazuwa a shafukan sada zumunta, yana mai cewa babu yadda zai yi bayani kan matsayin rashin lafiyar mutane saboda hakan ba daidai ba ne a likitance.

Me aka sani a kan alakar ibuprofen da Covid-19?

Babu wani bincike da ya alakanta ibuprofen da coronavirus (Covid-19).

Sai dai akwai wasu bincike da ke alakanta wasu cutukan numfashin da ibuprofen wanda ke cewa shan maganin na ta'azzara cutukan - ko da yake bamu sani ba ko ibuprofen din ne da kansa yake ta'azzara cutukan, a cewar Paul Little, wani farfesa kan kiwon lafiya a Jami'ar Southampton.

Wasu masana sun yi amannar cewa sinadaran da ke cikin ibuprofen masu rage radadi ka iya "durkusar" da garkuwar jikin mutane.

Farfesa Parastou Donyai ta Jami'ar Reading ta ce: "Akwai bincike da dama da suka nuna cewa yin amfani da ibuprofen ga cutar numfashi ka iya ta'azzara cutar ko ma ya haifar da wasu matsalolin na daban."

Amma ta ce, "Ban ga wata hujja ta kimiyya ba wacce ta bayyana karara cewa mutum dan shekara 25 wanda lafiyarsa kalau kuma ya sha ibuprofen saboda ya ga alamar COVID-19 zai fada cikin matsala ba."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Paracetamol ya kare a yawancin shagunan sayar da magani

Watsa labaran karya ya kawo rudani

Fargabar da ake nunawa game da amfani da ibuprofen ta sake fitowa fili a Faransa, bayan Jean-Louis Montastruc, wani likita a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Toulouse ya yi gargadi a Twitter cewa: "A wannan lokaci na coronavirus, yana da matukar muhimmanci a tuna amfani da magungunan rage radadi na ta'azzara zazzabi."

Wani sako da ministan lafiyar Faransa, Olivier Veran, ya wallafa a Twitter ya ce yin amfani da magungunan rage radadi "yana iya ta'azzara cutar" da mutum ke fama da ita kuma an yada sakon a Twitter fiye da sau 43,000.

Sai dai ya kara da yin kira ga mutane su tuntubi likita kafin daukar kowanne mataki.

Ana yayata wasu sakonnin Twitter cikin su har da wanda ke cewa ibuprofen "zai iya haifar da matsananciyar rashin lafiya a tsakanin kananan yara da manya mutane masu fama da rashin lafiya" wanda aka yayata shi fiye da sau 94,000 a Twitter.

Rashin masu matsaya iri daya daga wurin masana kiwon lafiya ya sa ana watsa labarai masu mabambantan ra'ayi da ma labaran karya a shafukan intanet, kuma jami'ai a dakin binciken kimiyya na Jami'ar Vienna sun wallafa wani bayani mai harshen damo a harshen Turancin Ingilishi da kuma Jamusanci.

Rahoton daga Rachel Schraer da Jack Goodman da kuma Alistair Coleman

Labarai masu alaka