Mikel Obi ya bar kungiyarsa bayan kalamansa kan Coronavirus

John Mikel Obi Hakkin mallakar hoto VI - Imgaes
Image caption Mikel Obi ya ce ba zai buga wasa a irin wannan yanayin ba na coronavirus

Tsohon kyaftin din tawagar Super Eagles ta Najeriya John Mikel Obi ya bar kungiyar Trabzonspor bisa amincewar bangarorin biyu 'yan sa'o'i bayan ya ce ya kamata a soke wasanni a gasar Turkish Super Lig ta kasar Turkiiyya saboda coronavirus.

Gasar Super Lig na daya daga cikin 'yan kalilan da ba su soke buga wasanni ba a Nahiyar Turai saboda yaduwar cutar, duk da cewa babu 'yan kallo ake buga wasannin.

Mikel Obi mai shekara 32, ya bayyana ra'ayin da ya ci karo da na hukumar kwallon kafar Turkiyya a shafinsa na Instagram.

A wani bayani da kulob din ya fitar ranar Talata ya ce dan wasan ya katse kwantaraginsa, sannan kuma ya hakura da albashinsa domin ya zama ba shi da kulob.

A ranar Asabar ne Obi ya rubuta a Instagram "akwai sauran abbubuwa a rayuwa fiye da kwallon kafa".

Sannan ya ce: "Ba na sha'awa kuma ba zan buga wasa a irin wannan yanayin ba."

"Ya kamata a ce kowa yana gida tare da iyalansa a wannan yanayin mai hadari. Ya kamata a dakatar da wasannin kakar bana yayin da duniya ke fuskantar tashin hankali."

Ra'ayin na Mikel Obi ya jawo martani na goyon daga tsofaffin 'yan kwallon da suka taka leda a Turkiyya: Radamel Falcao wanda ya ce "haka yake John", sai kuma Didier Drogba da ya ce "tabbas ka yi hangen nesa".

Mutanen da suka kamu da cutar a Turkiyya guda shida ne a lokacin da Mikel ya yi batun, duk da cewa yanzu sun kai 47.

Labarai masu alaka